Hukumar Tara Haraji ta tara Naira Tiriliyan 4.95 na haraji a 2020

32

Hukumar tara haraji ta tarayya ta ce ta tara tiriliyan 4 biliyan 952 da miliyan 243 da dubu 711 da 728 da digo 37 a matsayin kudaden haraji a shekarar kasafin kudi ta 2020.

Daraktan sadarwa na hukumar, Abdullahi Ahmad ne ya bayyana hakan a yau cikin wata sanarwa da ya fitar a Abuja.

Abdullahi Ahmad ya bayyana cewa wannan nasarar ta wakilci kusan kashi 98 cikin 100 na adadin kudin harajin kasa na naira tiriliyan 5 da Gwamnatin Tarayya ta sanya wa Hukumar Kula da Haraji ta Tarayya.

Daraktan ya nakalto Shugaban Hukumar, Muhammad Nami, yana cewa wannan aikin abin birgewa ne, idan aka yi la’akari da illar da cutar corona ta yi ga tattalin arzikin Najeriya.

Yayin da yake nazarin mahimmancin nasarar ta 2020, Muhammad Nami ya ce hukumar ta yi wannan bajinta ne a lokacin da farashin mai ya fadi kasa wanwar.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

nine + 7 =