Gwamnatin Tarayya zata bibiyi ranar komawa makaranta ta 18 ga watan Janairu

20

Ma’aikatar Ilimi ta Tarayya tace ranar 18 ga watan Janairu da aka tsara komawa makaranta, da wuya ta tabbata, a saboda haka akwai yiwuwar sanar da sabuwar rana, bisa la’akari da alkaluman cutar corona.

Ministan Ilimi, Adamu Adamu, ya sanar da haka a jiya a wajen taron manema labarai na kwamitin shugaban kasa mai yaki da corona, wanda aka gudanar a Abuja.

Ministan ya kara da cewa an tattauna akan matsalar a wajen zaman ganawar kwamitin da aka gudanar a jiya, kuma ma’aikatar zata dauki mataki a yau.

A wani labarin kuma, kungiyar malaman makaranta ta kasa ta bayyana cewa ta shirya tsaf domin komawa aiki, amma tayi gargadin cewa zata saka kafar wando daya da jihoshin da suka ki biyan malamai albashi tsawon watanni 4.

Kungiyar tace kasancewar malaman makaranta sun kwashe kimanin watanni 5 a gida saboda corona, zasu koma bakin aiki kasancewar sun san yadda zasu kare kawunansu.

Sakatare Janar na kungiyar, Mike Ene, ya sanar da haka a wata ganawa da manema labarai.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

one × 1 =