Gwamnatin tarayya, jihoshi da kananan hukumomi sun raba N619.34bn

42

Kwamitin Raban Arzikin Kasa a zaman ganawarsa na jiya ya raba jimillar naira biliyan 619 da miliyan 343 a matsayin azikin kasa na watan Disambar 2020 ga matakai uku na gwamnati.

Daga wannan adadin, Gwamnatin Tarayya ta karbi naira biliyan 218 da miliyan 297; jihohi sun karbi naira biliyan 178 da miliyan 280; Kananan hukumomin sun samu naira biliyan 131 da miliyan 792; yayin da jihohin da ke samar da mai suka samu naira biliyan 31 da miliyan 827 a matsayin kashi 13 cikin 100 na kudaden hakar ma’adinai.

Wata sanarwa da kakakin Ma’aikatar Kudi, Kasafin Kudi da Tsare-tsaren Kasa, Hassan Dodo, ya fitar a Abuja, ta kuma ce kudin tattarawa, aikawa da mayarwa ya haura Naira biliyan 59 da miliyan 147.

Kudaden da aka samu daga Harajin Kayayyaki ya kai naira biliyan 171 da miliyan 358 sabanin naira biliyan 158 da miliyan 785 da aka tara a watan da ya gabata.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

three − 3 =