Gwamnatin kasar Pakistan ta kaddamar da fatattakar jagororin gamayyar adawa ta PDM, inda take hukunta dayawa daga cikinsu bisa laifin shirya gangami a birnin Mardan.
Hakan yazo daidai lokacin da yan adawa ke shirin kara shirya zanga-zangar kin jinin gwamnatin Fira Minista Imran Khan, kamar yadda aka rawaito a jiya.
Imran Khan yana fuskantar babban kalubale kasancewar gamayyar PDM ta tsayar da ranar 31 ga watan Janairu a matsayin ranar karshe domin ya sauka ko kuma ya fuskanci dogon maci zuwa birnin Islamabad.
Jagororin PDM sun shirya gudanar da tattaunawa mai muhimmanci a yau a gidan tsohon Fira-Minista, Nawaz Sharif, dake birnin Lahore.
Majiyoyi sun ce shugaban jam’iyyar PPP, Bilawal Bhutto Zardari, ya isa birnin Lahore kuma zai gana da Maryam Nawaz, shugabar jam’iyyar PML-N, gabannin tattaunawar ta gamayyar PDM.