Dan takarar Shugaban Kasa a Uganda Bobi Wine yayi watsi da sakamakon zabe

101

Dan takarar adawa a Uganda, Bobi Wine ya ki amincewa da sakamakon da aka bayyana kawo yanzu inda ya kira kansa shugaban da aka zaba, duk da cewa hukumar zaben tace ba a kirga dukkan kuri’un ba tukunna.

Bobi Wine yayi zargin cewa zaben na jiya yaga mafi munin magudi a tarihin Uganda, amma bai bayar da wata hujja da zata tabbatar da ikirarin nasa ba.

Ya bayyana cewa yanzu gwagwarmaya ta fara.

Bobi Wine, wanda sunansa na gaskiya Robert Kyagulanyi, yace zai sake yiwa manema labarai jawabi a cikin ‘yan awanni kadan akan cigaban da aka samu.

Sakamakon farko dake shigowa daga hukumar zaben ya nuna Shugaba Yoweri Museveni yana kan gaba da sama da kashi 60 cikin dari.

Sojoji sun kewaye gidan Bobi Wine.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

3 × three =