Buhari ya taya Ahmad Lawan murna cika shekara 62 a duniya

141

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya taya Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Ahmad Lawan murna bisa cikarsa shekara 62 da haihuwa.

Buhari, a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun sa, Femi Adesina, ya fitar, ya yaba da dattako da kyakkyawan jagoranci da dan majalisar ya kawo a zauren majalisar, inda yace yana magance kowace matsala tare da kwarewar shekaru da hikima.

Shugaban yabi sahun mambobin jam’iyyar APC, majalisar kasa, ma’aikata, dangi, abokai da abokan Ahmad Lawan wajen murnar zagayowar ranar haihuwarsa.

Buhari, wanda yace cigaban da Ahmad Lawan ya samu a matakan shugabanci ya nuna tausayawarsa, tsayin daka da kuma mai da hankali kan inganta rayuwar ‘yan Najeriya, ya kara da cewa kyakkyawar dangantakar da ke tsakanin bangaren zartarwa da na majalisa ya bunkasa cikin gaggauwa tare da samar da kyakkyawan sakamako a cigaban kasar.

Yayi addu’ar Allah Madaukakin Sarki ya karawa Ahmad Lawan lafiya, hikima da tsawon rai don cigaba da yiwa kasa da mutane hidima.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

3 × five =