Buhari ya amince da nadin Fikpo a matsayin mukaddashin DG na NDE

32

Fadar shugaban kasa a yau ta sanar da cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da nadin Abubakar Fikpo a matsayin mukaddashin Darakta Janar na ma’aikatar samar da ayyukan yi ta kasa har zuwa lokacin da za a nada cikakken Darakta Janar.

Amincewar da shugaban kasar ya yi ya sabawa matsayin majalisar dattijai wacce a ranar 10 ga Disambar 2020, ta bukaci Buhari da ya soke umarnin da shugaban kasar ya bayar na korar Dakta Nasiru Argungu, a matsayin Darakta Janar na ma’aikatar samar da ayyukan yi ta kasa.

Korar Argungu a shekarar da ta gabata sakamakon rikice-rikicen da suka biyo bayan shirin Gwamnatin Tarayya na daukar ma’aikata dubu 774, Buhari ya umarci karamin Ministan Kwadago da Aiki, Festus Keyamo, wanda ke kula da hukumar, da ya zabi mukaddashin Darakta Janar na hukumar.

Babban mataimaki na musamman ga shugaban kasa kan harkokin yada labarai, Garba Shehu, a wata sanarwa a yau ya ce Buhari ya amince da nadin da Keyamo ya yi.

Kudurin da majalisar dattijai ta gabatar na neman Buhari ya dawo da Argungu ya biyo bayan bukatar da Sanatan da ke wakiltar Jigawa ta Gabas, Ibrahim Hassan Hadejia ya gabatar.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

4 × 2 =