An kashe Fulani 47 dauke da makamai a jihar Oyo

107

Jami’an operation burst, wanda suka hada da sojoji da yansanda sun kame wasu Fulani 47 dauke bindigogi da sauran makamai, a garin Igangan dake jihar Oyo.

An gano cewa an kama wadanda ake zargin a kusa da kogin Ofiki dake kusa da titin Tapa zuwa Igangan a yankin karamar hukumar Ibarapa ta Arewa a jihar.

Majiyoyi sun shaidawa manema labarai cewa ana zargin yan’uwan fulanin ne suka gayyato su domin kaddamar da hari, biyo bayan sumamen da yan kungiyar Amotekun suka kai a yankin a ranar Asabar.

Kungiyar Amotekun tace ta gudanar da sumame a maboyar masu garkuwa da mutane a yankin a ranar Asabar, lamarin da ya kai ga mutuwar mutane 3, yayin da daya daga cikin mutanenta ya samu rauni.

Kungiyar ta tsaro tace an gudanar da sumamen tare da hadin gwiwar yan kato da gora na kungiyar Miyetti Allah da mafarauta da sauransu.

Da aka tuntube shi, kakakin yansanda na jihar, Olugbenga Fadeyi, ya tabbatar da kamen.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

4 × four =