Shugaban Faransa Macron ya kamu da cutar corona

64

Fadar Shugaban Kasar Faransa tace Shugaban Kasa Emmanuel Macron ya kamu da cutar korona.

A wata sanawar da ta fito daga fadar tace shuganan dan shekaru 42 a duniya zai killace kansa na kwanaki bakwai.

Sanarwar ta bayyana cewa Mista Macron ya yi gwajin na korona bayan jikinsa ya fara nuna alamomin cutar.

Wani jami’in gwamnati yace har yanzu Shugaba Macron ne ke gudanar da mulki kuma zai ci gaba da aiki daga gida.

A wannan makon Faransa ta kakaba dokar hana fita cikin dare, domin taimakawa wajen rage yawan wadanda ke kamuwa da cutar.

Akwai mutane miliyan 2 da aka tabbatar sun kamu da corona a kasar, tun bayan farawar annobar, inda mutane sama da dubu 59 da 400 suka mutu, kamar yadda yazo a alkaluman jami’ar John Hopkins.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

14 − 1 =