Shugaba Buhari ya kara wa’adin kwamitin yaki da corona na shugaban kasa

16

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya gana da yan kwamitin yaki da corona na shugaban kasa.

Ganawar wacce aka gudanar a fadar shugaban kasa, tazo ne daidai lokacin da Najeriya ke yaki da dawowar annobar corona a karo na biyu.

Shugaban kasar a lokacin ganawar ya kara wa’adin kwamitin har zuwa watan Maris na 2021.

An kara wa’adin ne bisa la’akari da dawowar annobar corona a karo na biyu.

Shugaban kwamitin kuma sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha, a jiya ya sanar da sabbin ka’idojin yaki da bazuwa kwayar cutar, wadanda za suyi aiki zuwa makonni 5 masu zuwa.

Ya sanar da kulle dukkan mashaya, da gidajen wasannin dare da guraren taruka da na bukukuwa da na shakatawa.

Kazalika an rufe dukkan gidajen cin abinci, yayin da makarantu zasu cigaba da zama a rufe har zuwa akalla ranar 18 ga watan Janairun sabuwar shekara.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

fifteen − 7 =