Akalla mutane 26 aka kashe lokacin da wata fashewa ta girgiza filin jiragen saman Aden a kasar Yemen, jim kadan bayan saukar sabuwar gwamnati, a lamarin da wasu jami’ai suka bayyana da harin matsorata daga kungiyar yan tawayen Huthi dake samun goyon bayan kasar Iran.
Duk da kasancewar an bayar da rahoton cewa dukkan ministocin gwamnati basu ji rauni ba a harin, sama da mutane 50 ne suka jikkata, kuma akwai alamun za a samu karin wadanda suka mutu.
Hukumar agaji ta red cross tace daya daga cikin ma’aikatanta na daga cikin wadanda aka tabbatar da mutuwarsu, tare da karin wasu uku da suka samu raunuka.
Daidai lokacin da hayaki ke tashi daga ginin filin jiragen bayan fashewar ta farko, inda baraguzai suka warwatsu a wajen kuma mutane ke tururuwar zuwa duba wadanda suka samu raunuka, sai aka samu fashewa ta biyu.
Wani faifan bidiyo da kamfanin dillancin labarai na AFP ya dauka ya nuna wani abu mai kama da makami mai linzami ya daki hasumiyar filin jiragen saman, wanda a daidai lokacin yake makare da mutane, inda daga nan ya fashe.