Majalisar dinkin duniya ta sanar da tallafin dala miliyan 35 da dubu 600 domin fararen hular da fadan Habasha ya rutsa da su a yankin Tigray.
Majalisar dinkin duniya tace za ayi amfani da dala miliyan 25 wajen sayen magunguna domin fararen hula marasa lafiya da wadanda suka jikkata a Habasha, da kuma sayen abinci da ruwan sha.
Za ayi amfani da karin dala miliyan 10 da dubu 600 wajen samar da matsugunnai, da kiwon lafiya da ruwan sha, domin gomman dubban yan gudun hijira wadanda suka tsere zuwa kasar Sudan dake makotaka.