Majalisar Zartarwa ta amince da biliyan 44.5 domin ayyuka daban-daban

51

Zaman Majalisar Zartarwa ta Tarayya wanda Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya jagoranta ya amince da bayar da kwangiloli na naira biliyan 44 da rabi, domin ayyuka daban-daban a ma’aikatar ayyuka da gidaje da ma’aikatar wutar lantarki da ta babban birnin tarayya.

Majalisar ta kuma amince da naira biliyan 1 da miliyan 100 domin kammala gyaran wasu tituna a fadin kasarnan.

Ministan ayyuka da gidaje, Babatunde Fashola, ya sanar da haka lokacin da yake jawabi ga manema labaran fadar shugaban kasa a karshen zaman majalisar na bana.

Babatunde Fashola ya lissafa jihoshin da zasu amfana da suka hada da jihoshin Akwa Ibom, Anambra, Cross River, Nasarawa, Lagos, Ogun, Kogi, Edo, Yobe da Delta tare da babban birnin tarayya.

Ministan wutar lantarki, Sale Mamman, a nasa bangaren yace majalisar ta amince da sama da naira biliyan 4 da miliyan 700 domin bangaren wutar lantarki.

Ministan babban birnin tarayya, Mohammed Bello, yace majalisar ta amince da kwangilolin ruwan sha da tituna a birnin, wadanda kudinsu ya kai naira biliyan 31 da miliyan 600.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

eight − four =