Mahara sun kashe sama da mutane 100 a Habasha

35

Wasu mahara da ba a san ko su wane ne ba sun kashe sama da mutane 100 a wani kauyen jihar Benishangul-Gumuz da ke Habasha da safiyar Laraba.

Harin na zuwa ne kwana guda bayan Firaiministan kasar, Abiy Ahmed tare da manyan jami’an gwamnatin kasar da jami’an soji sun kai ziyara yankin domin tattauna batun yawan rikice-rikicen kabilancin da ake samu.

Wata malamar jinya a wani asibitin yankin da lamarin ya faru ta shaida wa manema labarai cewa akwai sama da mutane 30 da suka samu raunuka an kwantar da su a asibiti.

Wasu sun samu raunuka ne sakamakon harbin bindiga wasu kuma sun samu raunin ne sakamakon harin wuka.

Mai magana da yawun gwamnatin jihar, Beyene Melese, ya dora alhakin harin kan wadanda ya kira masu adawa da zaman lafiya.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

10 − three =