Fadar Shugaban Kasa na zargin ana shirin batawa Shugaba Buhari suna

19

Fadar shugaban kasa ta yi zargin cewa wasu abokan adawar gwamnati na siyasa suna shirin daukar nauyin gangamin yada labaran karya akan shugaban kasa Muhammad Buhari da nufin bata masa suna.

Kakakin shugaban kasa, Femi Adesina, a cikin wata sanarwa da aka aikawa dakunan yada labarai a jiya, yace za a kaddamar da gangamin batawa shugaba Buharin suna a internet, inda masu tsara shirin zasu nuna cewa shugaban kasar ba shine yake jan ragamar kasarnan ba.

Yayi zargin cewa tuni aka fara yada hakan daga wata kafa dake kasashen ketare.

Femi Adesina yace uban gidansa yayi kokari sosai a matsayinsa na shugaban kasar Najeriya, inda yayi ayyuka a bangaren tituna da hanyar jirgin kasa da gadoji da filayen jiragen sama, da sauran bangarori da dama, ya kara da cewa yayi kokari a bangaren gona.

Femi Adesina ya kara da cewa ana cigaba da yaki da rashawa da rashin tsaro da tayar da komadar tattalin arziki.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

3 × 2 =