EFCC ta samu nasarar kararraki 865 a kotuna a 2020

28

Mukaddashin shugaban hukumar yaki da rashawa ta EFCC, Mohammed Abba, yace hukumar ta samu nasara a kotuna sau 865 daga cikin kararraki dubu 1 da 305 da ta shigar a kotuna a bana.

Yace akwai jumillar korafe-korafe dubu 7 da 340 da ake bincike akai a halin yanzu, daga cikin korafe-korafe dubu 10 da 152 wanda hukumar ta karba.

Shugaban na EFCC ya kara da cewa hukumar ta kuma samu nasarar kwato kudade dayawa tare da kwace kadarori da dama daga hannun wadanda aka kama da laifin rashawa, bayan an bi matakin shari’ah.

Mohammed Abba ya sanar da hakan a jiya a sakonsa na karshen shekara, kamar yadda yazo a cikin wata sanarwa da kakakin hukumar ta EFCC, Wilson Uwajaren.

Da yake bayyana shekarar da muke ciki a matsayin ta musamman, Mohammed Abba ya kara da cewa hasashen EFCC wanda aka gina akan manufofi masu kyau, sun samu tsaiko saboda annobar corona.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

15 + eighteen =