
Bankin Duniya ya tattauna tare da Najeriya dangane da batun baiwa kasarnan bashi na shekaru biyar daga shekarar 2021 zuwa 2024, inda ya amince da bayar da bashin naira biliyan 1 da rabi domin taimakawa wajen farfadowa bayan annobar corona.
Bankin ya sanar da haka a yau cikin wata sanarwa da ya fitar a Abuja.
Bankin ya bayyana cewa Najeriya na cikin matsi da kuma faduwar da farashin mai yayi kasa wanwar, sanadiyyar corona, inda aka yi hasashen cewa tattalin arziki zai ragu da sama da kashi 4 cikin 100 a bana, lamarin da zai kara angiza kasarnan zuwa koma bayan tattalin arziki mafi muni tun na shekarun 1980.
A cewar bankin na duniya, kudaden shigar gwamnati zasu iya raguwa da sama da dala biliyan 15 a bana, kuma yanayin da ake ciki zai kara tunkuda karin yan Najeriya miliyan 5 zuwa talauci a bana.
Bankin duniyan yace bashin zai fi mayar da hankali a bangarori hudu, wadanda sune na gina dan’adam da karin samar da ayyukan yi da habaka tattalin arziki da fadada samar da kudaden shiga da inganta tushen aikin gwamnati.