Bama sha’awar komawa makaranta – Dalibin Kankara

36

Yan makarantar da aka sace a makarantar sakandiren kimiyya ta gwamnati dake Kankara a jihar Katsina, sun koka bisa wahalhalun da suka sha a wajen da aka boye su.

An sake su jiya a jihar Zamfara, inda aka kaisu Katsina a yau, cikin tsatstsauran tsaro.

A cewarsu, an ajiye su a cikin sanyi kuma suna cin abinci sau 1 cikin kwanaki 2.

Advertisement

A wani faifan bidiyo da ya bayyana a internet, daya daga cikin yaran da aka sace, Abubakar Salisu, yace dayawa daga cikin daliban basa fatan sake komawa makarantar da aka sace su.

Ya bayyana takaici kan wajen da makarantar take, wanda ya kawo cikas ga jami’an tsaro su cece su.

Abubakar Salisu yace suna jin kokarin da jami’an tsaro ke yi, a yunkurinsu na ceto su, a daya daga cikin guraren da aka ajiye su.

Advertisement

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

nineteen − 6 =