An kashe Mutane 11 a rikicin manoma da makiyaya a Chadi

26

An kashe mutane 11 a wani sabon rikici a kudancin kasar Chadi tsakanin manoma da makiyaya, a cewar mai gabatar da kara a yankin.

Fada ya auku a ranakun Lahadi da Litinin a wani kauye dake lardin gabas na Tanjile, bayan shanu sun lalata amfanin gona, lamarin da ya jawo manoma suka kai hari kan makiyaya.

Rikicin tsakanin manoma da Fulani makiyaya yana da tsohon tarihi a kudancin kasar Chadi, inda mutane da dama ke rike da bindigogi.

Mai gabatar da karar yace jami’an tsaro sun bude wuta akan manoma bayan sun hari motar yansanda da wani ofishi domin adawa da hukumomi wanda suna shiga tsakani wajen ceton makiyaya.

A watan Nuwamba, akalla mutane 22 aka kashe a rikice-rikice a lardin Kabbia, bayan wasu shanu sun tattake amfanin gona.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

four × two =