Alkalin alkalai na kasa, Mai Shari’ah Tanko Muhammad, ya kamu da cutar corona.
Wani alkali a kotun koli, Mai Shari’ah Ibrahim Saulawa, ya sanar da haka a yau a wajen bikin bude helkwata ta kasa ta kungiyar lauyoyi musulmai ta Najeriya, wanda aka yi a Abuja.
Yace alkalin alkalan na kasa na karbar magani a Dubai.
An lura cewa Mai Shari’ah Tanko Mohammed bai halarci zaman bikin bibiyar sabuwar shekarar ayyukan shari’ah na kotun koli ba, wanda aka yi a jiya, inda aka tsara cewa zai jagoranci rantsar da sabbin manyan lauyoyi guda 72 da suka samu mukamin SAN.