Mutane dubu 1 da 76 sun mutu sanadiyyar hadura cikin watanni 3

21

Hukumar kiyaye hadura ta kasa tace an samu hadura sau dubu 2 da 656 da mutuwar mutane dubu 1 da 76 a fadin kasarnan daga watan Yuli zuwa Satumbar bana.

Jami’in ilimintar da jama’a na hukumar, Bisi Kazeem, ya sanar da haka ranar Laraba yayin ganawa da manema labarai a Abuja.

Bisi Kazeem yace an samu haduran da mace-macen cikin watannin, inda ya kara da cewa hukumar baza tayi kasa a gwiwa ba a kokarinta na rage samun hadura akan manyan tituna.

Ya danganta yawancin haduran da mace-macen da aka samu akan hanyoyi daban-daban na kasarnan cikin watannin da gudun da ya wuce kima.

Bisi Kazeem ya bukaci masu ababen hawa da su hada kai da hukumar, inda yace hakan zai taimaka sosai wajen dakile yawaitar hadura akan tituna.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

five + 19 =