Mutane 6 sun mutu a Ivory Coast bayan kotu ta tabbatar da nasarar Ouattara

19

Rikici dangane da sake zaben shugaban kasar Ivory Coast, Alasanne Outtara ya jawo mutuwar mutane akalla 6, daidai lokacin da babbar kotun kasar ta tabbatar da cancatarsa ta tsayawa takara a karo na uku.

Alasan Watara mai shekaru 70 a duniya, ya samu kashi 94 cikin 100 na kuri’un da aka kada a zaben, amma ana zaman dardar a kasar ta Ivory Coast bayan jagororin yan adawa sun kauracewa zaben tare da shan alawashin kafa kishiryar gwamnati, domin adawa da zaben da suka ce haramtacce ne.

Akalla mutane 50 aka kashe a rikicin tun daga watan Augusta kuma aka kama manyan yan adawa 2, lamarin da ya haifar da fargabar cewa kasar ta Ivory Coast zata iya fadawa cikin gagarumin rikicin da ta shiga bayan zaben 2010 wanda ya jawo cece kuce.

Mazauna wani gari sun ce an kuma kashe karin wasu mutane 3 a tsakiyar Elibou a lokacin da aka gwabza tsakanin dakarun tsaro da masu zanga-zangar da suka katange wata babbar hanya.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

three × 4 =