
Yunkurin Shugaban Kasa Muhammadu Buhari na kayyade amfani da shafukan sada zumunta ya samu goyon baya a jiya bayan gwamnoni da sauran shugabanni daga yankin Arewacin Najeriya sun bayyana goyon bayansu ga yunkurin.
Gwamnatin Buhari ta mayar da kayyade shafukan sada zumunta a matsayin abinda tafi mayar da hankali akai, inda ta zargin shafukan na sada zumunta da yada labaran kanzon kurage, wanda tace zai iya jawo rushewar kasarnan idan ba a magance ba.
Kungiyar gwamnonin Arewa a zamansu na ranar Litinin sun bayyana goyon baya ga matakin na gwamnati, wanda suka ce, za a dauka ne da nufin magance yaduwar labaran karya a kasarnan.
Zaman ganawar da aka gudanar a gidan Sir Kashim Ibrahim dake Kaduna, ya samu halartar shugabanin majalisun sarakunan jihoshin Arewa 19 da sauran manyan masu ruwa da tsaki a yankin.
Kungiyar ta bayyana goyon bayan nata a takardar bayan taro da shugaban kungiyar, Gwamna Simon Lalong na jihar Filato ya bayar.