
Ministan Sufurin Jiragen Sama, Sanata Hadi Sirika, yace kwanannan gwamnatin tarayya zata fara rabon kudin ceto na naira biliyan 5, wanda ta amince a bawa masu harkar sufurin jiragen sama.
Hadi Sirika ya sanar da haka a wajen bude taron jin bahasin jama’a na kwanaki 3 akan kudirori 6 na majalisar zartarwa da aka kirkira da nufin fasalin hukumomin kula da sufurin jiragen sama a kasarnan.
Yace masu kamfanonin jiragen sama zasu samu naira biliyan 4 yayinda sauran masu kasuwancin bangaren sufurin jiragen sama za a basu naira billiyan 1.
Sai dai, majalisar dattawa tace kudaden baza su isa ba, wajen tabbatar da dorewar masu harkar sufurin jiragen sama.