Gwamnatin Tarayya ta sayi sabbin jiragen sama uku domin makarantar horas da matuka jiragen sama

42

Gwamnatin tarayya ta sayi sabbin jiragen sama guda uku domin makarantar horas da matuka jirgin sama.

Makarantar ita ce ta koyar da harkokin tukin jirgin sama dake Zaria a jihar Kaduna.

Ministan sufurin jiragen sama, Hadi Sirika, ya sanar da haka a ranar Lahadi ta shafinsa na Twitter.

Hadi Sirika yace babu wani aikin tukin jirgin sama da ya wuce samun ma’aikatan jiragen sama kwararru.

A cewarsa, aikin bayar da horon a yanzu sai zama mafi inganci, mafi sauri da kuma araha.

An samar da makarantar horas da matuka jiragen sama domin ta zama cibiyar horas da matuka jiragen sama na Najeriya da Afirka, da injiniyoyin kula da gyaran jiragen sama da kuma masana hanyar da jiragen sama suke bi.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

three × 3 =