Buhari ya bayar da umarnin sayar da kayan satar da aka kwace a watanni 6

47

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya amince da kafa wani kwamitin da zai yi aiki tsakanin ma’aikatu wanda aka dorawa alhakin sayar da kayayyaki da kadarorin da gwamnati ta kwace cikin watanni shida.

Babban lauyan kasa kuma ministan shari’ah, Abubakar Malami, ya sanar da haka jiya a Abuja lokacin da yake kaddamar da kwamitin mai wakilai 22.

Abubakar Malami ya bukaci kwamitin da ya gudanar da bincike da bibiya da kuma karbo kayayyakin sata da wadanda aka mallaka ta haramtacciyar hanya, bisa tanadin ka’idojin da ofishinsa ya fitar a bara.

Yace an kafa kwamitin a bisa umarnin shugaban kasa Muhammadu Buhari a watan Oktoban 2018 biyo bayan shawarwarin da kwamitin bin diddigin kashe kudade da kula da kayan satar da aka kwato ya bayar.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

five + twelve =