Buhari ya bayar da umarnin sanya masu yiwa kasa hidima a shirin inshorar lafiya

28

Darakta janar na hukumar matasa masu yiwa kasa hidima, NYSC, Brigadier Janar Shu’aibu Ibrahim, yace shugaban kasa Muhammadu Buhari ya umarci hukumar ta NYSC ta tabbatar da shigar da matasa masu hidinmtawa kasa a cikin shirin inshorar lafiya na kasa.

Shu’aibu Ibrahim ya sanar da cewa hukumar ta NYSC zata horas da matasa dubu 66 wadanda suka kamala manyan makarantu a fadin kasarnan domin bautawa kasa a rukunin B, wanda za a fara a yau.

Shu’aibu Ibrahim ya sanar da hakan a ranar Litinin lokacin da yake magana a wajen taron manema labarai a Abuja.

Darakta Janar ya bayyana shirin na bautawa kasa a matsayin wanda ake matukar bukata domin horas da matasan Najeriya kasancewar sune kan gaba wajen hadin kan kasa da cigaban ta.

Ya kuma gargadi wadanda suka kammala makaranta na bogi da ke neman kutsawa cikin sansanonin bayar da horon da su yiwa kansu kiyamul laili.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

7 − two =