
Hukumar lafiya matakin farko ta jihar Bauchi tace an samu barkewar zazzabin shawara a yankin karamar hukumar Ganjuwa ta jihar inda mutane 8 suka mutu bayan sun harbu.
Shugaban hukumar, Rilwanu Mohammed, ya sanar da haka ranar Litinin lokacin da yake zantawa da manema labarai a Bauchi.
Shugaban yace yawanci mutanen karamar hukumar manoma ne.
Rilwanu Mohammed yace hukumar zata fara rigakafin zazzabin nan bada jimawa ba a yankin karamar hukumar.
Shugaban hukumar ya roki mutane da kada su razana kasancewar zazzabin yana da rigakafi.
Ya kuma shawarci jama’a da suke amfani da gidan sauro a matsayin matakin kariya daga kamu da sauran nau’ikan zazzabi.