Zaman ganawar na ranar Laraba tsakanin gwamnatin tarayya da kungiyar malaman jami’o’i (ASUU) ya kare ba tare da an cimma matsaya ba.
Kungiyar ta ASUU a watan Maris ta ayyana tafiya yajin aiki biyo bayan adawar da take da yunkurin gwmanatin tarayya na tursasawa wajen amfani da tsarin biyan albashi na IPPIS.
An kuma tafi yajin aikin da nufin matsawa gwamnatin tarayya ta aiwatar da yarjejeniyar da aka cimma tsakanin kungiyar da gwamnatin tarayya a shekarar 2009.
Da nufin samo mafita a batutuwan da suka jawo yajin aikin, an gudanar da zaman ganawa daban-daban tsakanin dukkan bangarorin biyu.
Da yake zantawa da manema labarai a karshen zaman na ranar Laraba, Ministan Kwadago da Aikin Yi, Chris Ngige, yace gwamnatin tarayya baza ta iya biyan naira biliyan 110 da kungiyar ta ASUU ke bukata ba, domin farfado da jami’o’i.