Shugaban Kasar Kamaru Paul Biya yayi Allah wa dai da kisan yara bakwai yayin wani harbe-harben kan mutane dayawa a wata makaranta mai zaman kanta dake yakin a ake amfani da harshen turanci wanda ke fama da rikici.
Shugaban ya kira harbe-harben na ranar Asabar a matsayin abin takaici kuma cin zarafin da matsorata suka yiwa yaran da basu ji ba, basu gani ba.
Yace ya umarci hukumomin tsaro da su tabbatar da cewa dakaru da jami’an tsaro sun damke wadanda suka yi wannan mummunar aika-aikar domin a hukunta su.
Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya umarci hukumomi da su binciki harin tare da tabbatar da cewa an hukunta wadanda suke da hannu.