Osinbajo ya amince cewa miliyoyin yan Najeriya na fama da bakin talauci

26
Mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo

Mataimakin Shugaban Kasa Yemi Osinbajo ya amince cewa miliyoyin ‘yan Najeriya na fama da bakin talauci.

Yace shugabannin da aka zaba zasu zama na jeka na yi ka muddin basu hada kai ba wajen magance abinda da ya kira matsalolin dake neman tarwatsa kasarnan.

Osinbajo ya fadi hakan yayi bikin rufe taron wuni biyu tsakanin bangaren zartarwa da majalisa wanda aka gudanar a fadar shugaban kasa dake Abuja.

Yace akwai bukatar yan bangaren zartarwa da yan majalisa su hada kai muddin suna gudun bawa yan Najeriya kunya, wadanda suka basu damar rike mukaman siyasa a manyan matakai.

A takardar bayan taro da aka fitar a karshe taron, wadanda suka halarci taron, sun nemi a samar da shiri mai inganci na sansanta juna tsakanin bangaren zartarwa da na majalisa, domin cigaban kasa.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

three × five =