Ma’aikatan Poly sun bawa gwamnati wa’adin kwanaki 21 kafin su tafi yajin aiki

58

Manyan ma’aikatan kwalejojin fasaha wato polytechnic a kasarnan sun bayar da wa’adin kwanaki 21 kafin su tafi yajin aikin sai baba ta gani, muddin gwamnatin tarayya ta kasa magance matsalolin dake da alaka da tsarin biyan albashi na IPPIS.

Hakan na zuwa awanni 24 bayan kungiyar manyan ma’aikatan jami’o’i da kungiyar ma’aikatan makarantu wadanda basa koyarwa, suka tafi yajin aikin gargadi na kwanaki 14 bisa adawa da tsarin biyan albashi na IPPIS.

Da suke tashi daga taron ganawar gaggawa a Abuja, manyan ma’aikatan na polytechnic a karkashin kungiyarsu, sun bayyana rashin gamsuwa da yadda hukumar kula da ilimin fasaha take kula da tsarin aikinsu.

A takardar bayan taron da aka karantawa manema labarai a karshen taron, shugaban kungiyar na kasa, Philip Ogunsipe, yace daga cikin abubuwan da ma’aikatan ke korafi akai sun hada da kasa biyan karin kudi na sabon mafi karancin albashi da kudaden aiki mai hadari ga ma’aikatan lafiya dake kula da corona, da sauransu.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

2 × 5 =