Kungiyar ASUU ta soki Ministan Ilimi inda tace yayi murabus ya koma gona

21

Kungiyar Malaman Jami’o’i (ASUU) ta shawarci karamin ministan ilimi, Chukwuemeka Nwajuiba, da yayi murabus ya koma gona.

Shugaban kungiyar na reshen jami’ar Ibadan, Farfesa Ayo Akinwole, ya sanar da haka a Ibadan lokacin da yake mayar da martani dangane da sukar da ministan ya yiwa kungiyar.

Yace sukar da minista ta nuna cewa shi ba masani bane a harkokin ilimi.

Ministan, yayin wata ganawa a ranar Litinin, yace kamata yayi malaman jami’o’in dake yajin aiki su koma gona, inda yace baza su tsarawa wanda ya dauke su aiki yadda za a biya su albashi ba.

Amma Akinyole ya bayyana jawabin na Nwajiuba da cewa ya nuna yadda ya jahilci sana’ar koyarwa da kuma yadda gwamnati mai ci ta ke yiwa harkar ilimi rikon sakainar kashi.

Kungiyar ta ASUU a ranar 23 ga watan Maris ta fara yajin aikin sai baba ta gani domin tursasawa gwamnatin tarayya ta aiwatar da yarjejeniyarta da lakcarori da kuma adawa da tsarin biyan albashi na IPPIS.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

eighteen − 3 =