An wawashe gidajen ajiya 4 a Abuja

22

Bata gari sun wawashe kayayyaki a gidajen ajiya sama da guda 4 a fadin Abuja, cikin awanni 48 da suka gabata.

Rikicin, wanda ya samo asali daga harbin masu zanga-zangar da basa dauke da makamai, a Lekki tolget dake Lagos a ranar Talatar da ta gabata, yayi saurin bazuwa zuwa sauran sassan kasarnan, inda ake harar gidajen ajiya na gwamnati da na yan kasuwa, tare da gidajen manyan jami’an gwamnati.

Babban Birnin Tarayyar yaja hankalin masu wasoson kayan, wadanda a ranar Lahadi da rana suka mamaye gidajen ajiya a rukunin masana’antu dake Idu, inda suka kwashe kayayyaki da suka hada da babura da buhunan shinkafa da gari da kuma atamfofi.

A jiya da safe, masu wasoson sun kuma sake haduwa a Idu inda suka kai farmaki zuwa wani gidan ajiyar.

Zuwa lokacin hada wannan rahoton, wasoson kayan ya bazu zuwa yankin Gwagwalada, inda masu kwashe kayan suka wawashe gidan ajiyar kayan tallafin corona.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

3 × 1 =