Akalla mutane 21 ake kyautata zaton sun mutu a tashin hankalin da ya biyo bayan zaben kasar Guinea da aka gudanar a farkon watan nan wanda kuma ake takaddama a kai.
An cigaba da arangama tsakanin magoya bayan yan adawa da jami’an tsaro a karshen mako, lokacin da hukumar zabe ta tabbatar da nasarar shugaban kasa Alpha Conde a zango na uku wanda ya jawo cece kuce.
Jam’iyyar adawa da ta ayyana kanta a matsayin wacce ta lashe zaben, tace Alpha Conde ya karya doka lokacin da ya sauya kundin tsarin mulki a watan Maris, domin bawa kansa damar sake tsayawa takara.
Majalisar Dinkin Duniya da Kungiyar Tarayyar Afirka sun aika da masu shiga tsakani zuwa kasar ta Guinea domin kokarin sasantawa.