Abin da ya sa cutar sanƙarau ke tasiri a Arewacin Najeriya

40

Cutar sanƙarau, cuta ce wadda ta daɗe tana yin illa musamman ga ƙananan yara a Najeriya a wani lokacin kuma ta kashe su, kuma akasarin waɗanda take yi wa illa daga arewacin ƙasar suke.

Hukumar da ke yaƙi da cutuka masu yaɗuwa a ƙasar wato NCDC ta bayar da rahoton cewa cutar ta kashe mutum aƙalla 269 tun daga farkon wannan shekara.

Baya ga kisa, wasu daga cikin illolin da cutar take yi wa waɗanda suka kamu da ita sun haɗa da makanta, da kurmancewa da farfaɗiya da wasu ciwuka na daban.

Yin riga-kafi na daga cikin hanyoyin da ke magance cutar, sai dai rashin riga-kafin a Najeriya na daga cikin abubuwan da suka sa ake samun ɓarkewar wannan cuta a ƙasar, kamar yadda Dakta Salisu Abdullahi Balarabe ya bayyana, wanda farfesa ne kan fannin lafiyar ƙwaƙalwa da laka a asibitin koyarwa na Usumanu Ɗanfodio da ke Sokoto.

Farfesan dai ya gudanar da bincike kan yadda wannan cutar ta yi wa mutanen ƙasar illa a shekara 100 baya kuma a tattaunawarsa da BBC, ya yi ƙarin bayani kan cutar.

Me ya sa cutar sanƙarau ke tasiri za Najeriya?

A cewar Dakta Salisu, “Ana gudanar da riga-kafin cutar sanƙarau a Najeriya ne a duk shekara, kuma ana yin wannan riga-kafin ne kawai a lokacin da aka samu ɓarkewar cutar”.

“Amma a ganina, a 2018, gwamnatin ƙasar ta saka riga-kafin sanƙarau a cikin shirye-shiryenta na riga-kafin cutuka, amma wannan shirin bai yi tasiri ba kuma bai kai wasu sassan ƙasar ba.”

A cewarsa, shirin riga-kafin ya ƙi tasiri ne sakamakon tsadar da yake da shi, kuma riga-kafin da aka fito da shi an fito da shi ne domin magance nau’i guda kawai na sanƙarau ɗin a maimakon nau’uka daban-daban.

Ya ce a shekara biyu zuwa uku da suka wuce, wani na’ui na daban suke gani na sanƙara’u ɗin ba nau’in da ake yin riga-kafin domin shi ba ne.

Sai dai ya ce mafita a nan ita ce, idan ana so riga-kafin ya yi aiki, ya kamata a samo riga-kafin da zai magance nau’uka aƙalla huɗu na wannan cuta ba wai nau’i ɗaya ba.

Me ke jawo cutar?

A cewar Dakta Salisu, manyan abubuwan da ke jawo cutar sanƙarau suna da alaƙa da abu biyu ne, na farko sauyin yanayi na biyu kuma muhalli.

A cewarsa, Arewacin Najeriya ne cutar ta fi ƙamari, da kuma ƙasashe kamar su Senegal da Ethiopia.

Bincike da masana da dama suka gudanar ya nuna cewa saboda yanayin zafi da ake samu a wasu yankunan na ƙara taimakawa wurin samun wannan cuta.

Dakta Salisu ya ce cutar kuma na yaɗuwa a lokacin hunturu tsakanin Nuwamba zuwa Maris har wani lokaci ma zuwa Yuni.

“A wannan lokaci, akwai wata ƙwayar cuta da ke yawo da ake kira Influenza, waɗanda ke ɗauke da cutar Meningococcal a jikinsu sai ta farfaɗo ta shiga cikin jininsu, daga jini sai ta wuce ƙaƙwalwa zuwa laka,

Hanya ta biyu kuma da ake kamuwa da cutar in ji Dakta Salisu ita ce yadda ake samun cunkoson mutane a muhalli ko kuma rashin tsaftaccen muhallin shi kansa.

BBC Hausa

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

5 × three =