Yansanda a Kano sun kama wasu mutane biyu da ake zargi da kisan likitan gashin kashi, Atiku Tijjani Shu’aibu

400

Yansanda a Kano sun ce sun kama wasu mutane biyu da ake zargi suna da hannu a kisan wani likitan gashin kashi mai suna Atiku Tijjani Shu’aibu Ringim, wanda aka kashe saboda wayar hannu a jihar.

Kakakin yansanda, Abdullahi Haruna Kiyawa ya sanar da haka ga SkyDaily ranar Asabar.

Yan daban a ranar Alhamis da misalin karfe 8 na dare aka yi zargin sun kaiwa Atiku Tijjani hari inda suka kashe shi lokacin da suke kokarin kwace masa wayarsa.

Lamarin da ya jawo mutuwar Atiku Tijjani, ma’aikaci a Asibitin Koyarwa na Mallam Aminu Kano, an ce ya auku lokacin da yaje kai wa abokinsa ziyara a kusa da Jan Bulo dake kan titin Gwarzo a kwaryar birnin Kano.

Haruna Kiyawa yace ana cigaba da binciken mutane biyun da aka kama suna da hannu a lamarin kuma suna bawa yansanda bayanai masu muhimmanci.

Sai dai, tuni aka binne gawar mamacin a garinsu na Ringim dake jihar Jigawa, bisa koyarwar addinin Islama.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

eighteen − sixteen =