Shugaba Buhari ya kare ciyo basussukan da gwamnatinsa ke yi

33

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya kare ciyo bashin da gwamnati ke yi domin samar da kudaden gine-gine, inda ya tabbatar da cewa gwamnatinsa ta ciyo basussuka domin cigaban kasarnan wajen magance karancin ababen more rayuwa.

Da yake jawabi a wajen ganawa ta bidiyon kai tsaye tare da ‘yan kwamitin shugaban kasa na bayar da shawara kan tattalin arziki wanda aka gudanar a fadar shugaban kasa dake Abuja, Shugaba Buhari yace dole kasarnan ta gyara titunanta domin kare rayuka daga hadarurruka.

Ya bayyana takaicin cewa gazawa wajen samar da tituna domin sufuri mai tsafta, ya hana kasarnan zama cibiyar sufurin jiragen saman kaya da kuma shigo da kaya ta jiragen ruwa, a Afirka ta Yamma.

Dangane da batun tattalin arziki, Shugaba Buhari ya tabbatar da kalubalen da ake fuskanta bisa faduwar farashin danyen mai da kuma matakin da gwamnati ta dauka na bin umarnin kungiyar kasashe masu arzikin mai, OPEC, na rage yawan man da ake hakowa.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

11 − eight =