Gwamnatin tarayya ta sanar da sake bude dukkan filayen jiragen sama masu zirga-zirga a cikin kasa.
Ministan sufuri, Hadi Siriki, ya sanar da haka a wajen taron manema labarai na kwamitin shugaban kasa kan cutar corona.
Hakan yazo bayan a cewarsa har yanzu dukkan jiragen shata sai sun samu sahalewa kafin suyi aiki.
A cewarsa, za a bude sauran filayen jiragen sama masu zaman kansu bayan sun cimma dukkan ka’idoji da dokokin cutar corona da kuma sahalewar hukumar kula da sufurin jiragen sama ta kasa.
Sai dai, ya kara da cewa ana cigaba da tattaunawa akan sake bude sararin saman Najeriya domin wasu jiragen sama da kasashe da aka haramtawa shigowa Najeriya.
Gwamnati ta sanar da cewa za ayi amfani da tsarin ramuwar gayya ga dukkan kasashen da suka hana shigowar jiragen sama daga Najeriya.