Gwamna Matawalle na Zamfara ya samu sarautar gargajiya ta Ife

80

Sarkin Ife, Oba Adeyeye Enitan Ogunwisi, ya bawa Gwamnan Jihar Zamfara, Bello Mohammed, Matawallen Maradun, sarautar gargajiya mai suna “Obapero na Ife-Odua”

Sarkin ya sanar da bayar da sarautar ga gwamnan lokacin da ya kai masa ziyara zuwa gidansa dake Abuja a ranar Juma’a.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa dauke da sa hannun mai bawa gwamnan shawara na musamman kan wayar da kan jama’a da yada labarai, Zainali Baffa, wacce aka bawa jaridar SkyDaily ranar Juma’a.

Kamar yadda yazo cikin sanarwar, sarautar wacce ke nufin mai samar da zaman lafiya, za a bawa gwamnan ita nan da makonni kadan masu zuwa.

Sanarwar ta kara da cewa Sarkin ya yaba da kyawawan halayen Gwamna Matawalle, a matsayinsa na shugaba mara kabilanci kuma dan siyasa, inda yayi nuni da cewa kyawawan manufofinsa sune suka jawo nasarar da ya samu wajen dawo da zaman lafiya ga jihar da ya gada mai cike da rikici.

Sarkin yace shirye-shiryen Gwamna Matawalle na garanbawul a bangaren hakar ma’adanai a jihar, matakine na jarumta wanda babu kamarsa, kuma zai habaka arzikin kasarnan.

Da yake mayar da martani, Gwamna Matawalle ya bayyana godiyarsa ga sarkin bisa sarautar da aka bashi, inda yayi alkawarin zuwa Ife da zarar ya samu hali, domin bikin nadin sarautar.

Gwamna Matawalle yace da sabon tsare-tsaren gina bangaren hakar ma’adanai da gwamnatinsa ke yi, cikin watannin kadan masu zuwa, jihar Zamfara zata zama daga cikin jihoshi mafiya arziki a fadin kasarnan.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

2 × five =