Corona: Merkel za ta gana da gwamnoni

25
Angela Markel

Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta nemi ganawa da gwamnoninin kasar 16 domin tattauna matakai na gaba kan yaki da yaduwar annobar corona tsakanin al’umma.

Sama da mutane 2,000 cutar Corona ta kama a makonni biyu na baya-bayan nan a cewar hukumin kasar Jamus, sabanin daruruwa da ake samu a watannin Mayu zuwa Yuni.

Taron shugabannin da zai gudanar ta internet, zai mayar da hankali kan matsayar makarantu da wuraren kasuwanci da rage adadin taron jama’a ko bukukuwa a cikin gida, inda adadin mutane daga 25 zuwa 50 kacal ne kawai za su rinka taruwa.

Hukumomin lafiya a Jamaus sun yi gargadin cewa yawan taron jama’a da sauran shagulgula ne ummul aba’aisin karuwar cutar.

DW

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

4 × 5 =