Buhari ya nemi sahalewar majalisa wajen biyan N148B ga jihoshi 5

23
Muhammadu Buhari

Shugaban Majalisar Dattawa Sanata Ahmad Lawan yayi tsokacin cewa Shugaban Kasa Muhammadu Buhari zai aika da kasafin kudin badi zuwa majalisar kasa a mako mai zuwa.

Ya kuma yi nuni da cewa Shugaba Buhari a yau ya bukaci majalisar kasa da ta amince da sakin kudi naira biliyan 148 da miliyan 100 domin a biya jihoshin Ondo da Rivers da Cross-River da Osun da Bayelsa.

Shugaba Buhari a wasikarsa, wacce shugaban majalisar dattawa ya karanta, yace za a biya kudaden saboda gina titunan gwamnatin tarayya a jihoshinsu.

Rabe-raben kudaden ya hada da naira biliyan 78 da miliyan 900 na jihar Rivers, sai biliyan 38 da miliyan 400 na jihar Bayelsa, da biliyan 18 da miliyan 300 na jihar Cross River, sai biliyan 7 da miliyan 800 na jihar Ondo da kuma naira biliyan 4 da miliyan 500 na jihar Osun.

Yace majalisar zata ware watan Oktoba domin kare kasafin kudi, yayin da zasu tsayar da watan Nuwamba domin aikin bibiyar kunshin kasafin kudin.

A wani cigaban makamacin wannan kuma, Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya aikawa da majalisar wakilai ta kasa wasika yana neman a salahewa gwamnatin tarayya ta biya jihoshi biyar kudaden gina tituna a madadin ta.

Kakakin majalisar, Femi Gbajabiamila, ya karanta bukatar shugaban kasa a lokacin bude zaman majalisar na ranar Talata.

Shugaba Buhari yayi nuni da cewa majalisar zartawa ta gwamnatin tarayya a zamanta na ranar 3 ga watan Yunin bana, ta amince da biyan kudaden.

Kakkakin majalisar ya kuma karanta shafin farko na dokar masana’antar man fetur wacce Shugaba Buhari ya aika zuwa majalisar kasa, a lokacin hutun yan majalisar na shekara-shekara wanda ya shafe watanni biyu.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

eight + 8 =