Kotun kundin tsarin mulki a Ivory Coast ta haramtawa tsohon shugaban kasar Laurent Gbagbo da tsohon Fira-Minista Guillaume Soro, tsayawa takara a zaben shugaban kasar da za ayi wata mai zuwa.
Tun a baya hukumar zabe tace zata haramta tsayawa takara ga dukkan wanda yake da tarihin aikata laifi.
Dukkan mutanen biyu suna da hukunce-hukuncen da aka yanke musu.
Tun da farko, zanga-zanga ta barke a birane da dama bisa matakin shugaban kasa Alassane Ouattara na tsayawa takara a karo na uku, abinda kundin tsarin mulkin kasar ya haramta.
Mutane 15 sun mutu a rikicin tun bayan da yace zai sake tsayawa takara a watan da ya gabata.
Ya yanke shawarar tsayawa bayan wanda ya zaba a matsayin magajinsa yayi mutuwar bazata a watan Yuli.