
Shugabannin Kasashen Yammacin Afrika, sun nuna alamun fara sassauta takunkumin da suka sakawa kasar Mali, bayan juyin mulkin da aka yi a kasar a watan da ya gabata.
Jakada na musamman da Kungiyar ECOWAS ke turawa zuwa Mali domin sasanci, tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan, ya bayyana cewa sojojin da suka hambarar da Shugaba Boubacar Keita sun fara jin kiran da kasashen duniya ke yi musu na mulkin Dimokradiyya.
Wannan kalaman na Goodluck Jonathan, wasu alamu ne da ke nuna cewa akwai yiwuwar kungiyar ECOWAS ta amince da nadin tsohon ministan tsaro na kasar, Bah Ndaw a matsayin shugaban kasa na riko, inda kuma wanda ya jagoranci juyin mulkin na Mali, Kanal Assimi Goita zai zama mataimakin shugaban kasa.
An daina shiga da kayayyaki zuwa Mali tun bayan takunkumin da ECOWAS ta kakabawa kasar ta Mali.