Shugabannin sojin da suka yi juyin mulki a Mali sun tattauna da ‘yan hamayya bayan tumbuke Shugaba Ibrahim Boubacar Keïta

35

Shugabannin sojin da suka yi juyin mulkin ranar Talata a kasar Mali sun tattauna da shugabannin ‘yan hamayyar kasar wadanda suka yi maraba da tumbuke gwamnatin Shugaban Kasa Ibrahim Boubacar Keïta.

Yan hamayyar sun dorawa Ibrahim Keïta alhakin gaza dakatar da hare-haren masu ikirarin jihadi da kuma tabarbarewar tattalin arzikin kasar.

Gamayyar ‘yan hamayyar ta ce ta yaba da kishin da sojin suka nuna wajen son kafa gwamnatin rikon kwarya ta farar hula.

Wani kanal na rundunar sojin kasar, Assimi Goita, shi ne ya zama shugaban mulkin sojin.

Ya bukaci ma’aikata su koma bakin aiki. Amma kwamitin tsaro na majalisar dinkin duniya yayi Allah wadai da juyin mulkin.

Shugabannin kasashen Afirka ta yamma karkashin ECOWAS sun sanar da kakaba wasu takunkumai kuma zasu gudanar da wata ganawa ta bidiyo a yau domin tattauna karin matakan da za a dauka.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

3 × two =