NAPTIP ta kama Kwamandan Hisbah da Dagaci a Kano bisa zargin sayar da wani yaro

48

Ofishin hukumar hana safarar mutane ta kasa (NAPTIP) na shiyyar Kano ya kama wasu mutane uku a Kano bisa zargin sayar da wani yaro dan shekara daya a jihar Imo.

Wadanda ake zargin sune kwamandan Hisbah na Fagge, Jamilu Mohammed, da dagacin Fagge, tare da wata mata mai suna Loveth wacce ta sayi yaron.

Shugaban ofishin NAPTIP na shiyyar, Shehu Umar, ya gayawa manema labarai cewa an gayyaci wadanda ake zargin domin amsa tambayoyi dangane da lamarin.

An gano cewa yaron da aka sayar, iyayensa ne suka jefar da shi, kuma ake kula da shi a hukumar Hisbah.

Sai dai, an zargin kwamandan Hisbah ya hada baki da dagacin inda suka sayar da shi.

A cewar shugaban NAPTIP, yaron wanda ake zargin kwamandan Hisbah tare da dagacin Fagge sun sayar da shi ga Loveth, a ceto shi daga hannun mahaifiyar Loveth a jihar Imo.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

3 − one =