
Shugabannin addinai a jihar Kaduna sun bayyana masu aikata fyade a matsayin yan ta’adda wadanda ya kamata a tsaurarawa hukunci domin ya zama izina ga wasu.
Yayin da shahararren malamin addinin musulunci, Sheikh Kabiru Haruna Gombe ya bayar da shawarar zartar da hukuncin kisa ga masu aikata fyade, shugaban kungiyar kiristoci ta kasa CAN reshen jihar Kaduna, Reverend John Joseph Hayab, yace dole a hukunta masu aikata fyade bisa dokokin kasa.
Malaman addinan, wadanda suka yi jawabi a wajen wani taro na wuni biyu akan daukar mataki dangane da fyade, sai dai, sun yi nuni da cewa dabi’ar na da hannu wajen rashin tsaron dake addabar kasarnan.
A cewar malamin addinin musuluncin, masu aikata fyade yan ta’adda ne kuma ya kamata ake zartar musu da hukuncin kisa kamar yadda ake yi a kasashen irinsu India da China da Masar da Iran.
A nasa bangaren, shugaban na CAN yace fyade na taka muhimmiyar rawa ga kalubalen tsaro da Najeriya ke fuskanta a yanzu.