Majalisar Zartarwa ta Tarayya ta amince da biliyan 3.9 domin kammala sakatariyoyin tarayya

19

Majalisar zartarwa ta tarayya ta amince da kashe karin kudi naira biliyan uku da miliyan dari tara domin kammala ayyukan gina sakatariyoyin gwamnatin tarayya a jihoshin Anambra da Bayelsa da Nasarawa da Zamfara da kuma Osun.

Majalisar ta kuma amince da fitar da kudi naira biliyan daya da miliyan dari domin sake gyaran sashe na biyu na madatsar ruwa ta Usama dake Bwari a babban birnin tarayya, Abuja.

Ministan ayyuka da gidaje, Babatunde Fashola, tare da ministan babban birnin tarayya, Muhammed Bello, suka tabbatar da hakan a wajen taron manema labarai dangane da abubuwan da aka cimma a zaman majalisar, karkashin jagorancin shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Fashola ya sanar da cewa aikin sakatariyoyin an bayar da shi tunda farko a shekarar 2011 akan kudi naira biliyan goma sha uku da miliyan dari biyar, inda yace kudin da aka amince na naira biliyan uku da miliyan dari tara na karashen ayyuka ne domin dukkan sakatariyoyin guda biyar, wanda ya kawo jumillar kudin ayyukan zuwa naira biliyan goma sha bakwai da miliyan dari hudu.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

7 + 6 =