Juyin Mulki: Tawagar ECOWAS karkashin shugabancin Goodluck Jonathan sun isa Mali

45

Shugabannin ECOWAS sun sauka a Mali ranar Asabar, a kokarin matsin lamba domin gaggauta komawa mulkin farar hula, bayan juyin mulkin soja wanda ya tumbuke shugaban kasa Ibrahim Boubacar Keita.

Tawagar, karkashin shugabancin tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan, na shirin ganawa da sabbin shugabannin mulkin sojin, da kuma hambararren shugaban kasar.

Sojojin da suka yi tawaye sun dauke Ibrahim Keita tare da sauran shugabanni bayan sun yi tawayen ranar Talata, lamarin da ya kara tabarbara zaman lafiyar kasar wacce tuni take fama da rikicin masu ikirarin jihadi da kuma rashin amincewa da gwamnati.

Makotan Mali sun nemi a mayar da Ibrahim Keita kan karagar mulki, inda suka ce manufar ziyarar tawagar shine taimakawa wajen tabbatar da gaggauta dawowar doka da oda.

Wani jami’in tawagar ya gayawa SkyDaily cewa zasu gana da shugabannin mulkin sojin, daga baya su gana da Ibrahim Keita, wanda yake tsare tare da Firai-Minista Boubou Cisse a Kati, wani barikin soja da aka kwace, inda kuma daga nan aka kaddamar da juyin mulkin.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

3 × two =