Gwamnatin tarayya ta matsar da ranar dawowa jigilar jiragen sama na kasa da kasa, ciki da wajen Najeriya, daga gobe zuwa 5 ga watan Satumba.
Ministan sufurin jiragen sama, Hadi Sirika, ya fada a ranar 17 ga watan Augustan da muke ciki cewa za a dawo da jigilar jiragen saman kasa da kasa a gobe, biyo bayan matsawar da jama’a ke yiwa gwamnati akan a dawo da jigilar.
Amma a taron manema labarai na kwamitin shugaban kasa kan cutar corona na jiya, wanda aka gudanar a Abuja, shugaban hukumar sufurin jiragen sama, Musa Nuhu, ya ayyana cewa ba za a samu dawo da jigilar jiragen saman kasa da kasa ba, kamar yadda aka sanar a baya.
Yace an zabi ranar 5 ga watan Satumba a matsayin sabuwar ranar dawowa jigilar jiragen sama, inda ya tabbatar da cewa har yanzu akwai matsalolin da za a gyara kafin a a bawa kamfanonin jiragen saman kasa da kasa damar su fara shigowa ko fita daga Najeriya.